105.The Elephant

  1. Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa* ba
  2. Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba
  3. Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a
  4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta
  5. Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye