110.Divine Support

  1. Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara
  2. Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya-ƙungiya
  3. To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne