114.Mankind

  1. Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne
  2. Mamallakin mutane
  3. Abin bautãwar mutãne
  4. Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa
  5. Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane
  6. Daga aljannu da mutane