15.The Rock
- L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa
- Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi
- Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani
- Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne
- Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba
- Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne
- Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya
- Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,* bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba
- Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi
- Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka
- Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi
- Kamar wancan ne Muke shigar da shi* a cikin zukãtan mãsu laifi
- Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige)
- Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa
- Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce
- Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo
- Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa
- Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi
- Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli
- Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã* da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba
- Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne
- Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba
- Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada
- Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri
- Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani
- Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja
- Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar* iskar zafi
- Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja
- To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa* a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada
- Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya
- Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar
- Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba
- Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja
- Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne
- Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako
- Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su
- Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri
- Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sanan ne
- Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya
- Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake
- Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici
- Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu
- Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya
- Tanã da ƙõfõfi bakwai,* ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe
- Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa
- Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu
- Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã
- Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikin ta ba
- Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai
- Kuma azãbãTa ita ce Azãba mai raɗaɗi
- Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm
- A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne
- Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani
- Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra* ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara
- Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni
- Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijin sa, fãce ɓatattu
- Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni
- Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi
- Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya
- Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka
- To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu
- Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba
- Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa
- Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne
- Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku
- Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga Asuba
- Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra
- Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni
- Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki
- Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba
- Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna* idan kun kasance mãsu aikatãwa ne
- Rantsuwa da* rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa
- Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã
- Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu
- Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali
- Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya
- Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni
- Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika* sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci
- Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani
- Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri* sun ƙaryata Manzanni
- Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su
- Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu
- Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba
- Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba
- Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau
- Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani
- Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu* da Alƙur'ãni mai girma
- Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni
- Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne
- Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa
- Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi
- To, rantsuwa da Ubangijinka!* Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya
- Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa
- Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki
- Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu* izgili
- Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani
- Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili)
- Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada
- Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka