19.Mary

  1. K̃.H. Y.I. Ṣ̃
  2. Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya
  3. A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye
  4. Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji
  5. Kuma lalle nĩ, na ji tsõron* dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa
  6. Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji
  7. (Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni
  8. Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa
  9. Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba
  10. Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai
  11. Sai ya fita ga mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma
  12. Yã kai Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro
  13. Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gun Mu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa
  14. Kuma mai biyayya ga mahaifan sa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba
  15. Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai
  16. Kuma ka ambaci Maryamu* a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas
  17. Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci
  18. Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini
  19. Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki
  20. Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba
  21. Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi* ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce
  22. Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa
  23. Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta
  24. Sai (yãron da ta haifa) ya* kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki
  25. Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu
  26. Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki*. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba
  27. Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma
  28. Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba
  29. Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri
  30. Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi
  31. Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai
  32. Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri
  33. Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai
  34. Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta
  35. Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã*. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa
  36. Kuma lalle Allah ne Ubangijina* kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici
  37. Sai ƙungiyõyin* suka sãɓã wa jũna a tsakãnins u. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma
  38. Mẽne ne ya yi jinsu*, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna
  39. Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni
  40. Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa* da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su
  41. Kuma ambaci Ibrãhĩm* a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi
  42. A lõkacin da ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka
  43. Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici
  44. Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama
  45. Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan
  46. Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci
  47. Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka.* Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni
  48. Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina
  49. To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi
  50. Kuma Muka yi musu kyauta daga Rahamar Mu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya* maɗaukaki
  51. Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi
  52. Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa
  53. Kuma Muka yi masa kyauta daga Rahamar Mu da ɗan'uwan sa Hãrũna, ya zama Annabi
  54. Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi
  55. Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens *da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa
  56. Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi
  57. Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki
  58. Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka
  59. Sai waɗansu 'yan bãya* suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri
  60. Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme
  61. Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa
  62. Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice
  63. Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa
  64. (Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka* Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma** (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba)
  65. Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãnin su. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautar sa. Shin kã san wani takwara a gare shi
  66. Kuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai
  67. Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba
  68. To, Munã rantsuwa da Ubangijin ka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne
  69. Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya
  70. Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗan da suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita
  71. Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata.* Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce
  72. Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne
  73. Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa
  74. Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã
  75. Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna
  76. Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma
  77. Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya
  78. Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne
  79. Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa
  80. Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai
  81. Kuma suka riƙi gumãka,* baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su
  82. Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu
  83. Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu* a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa
  84. Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar Ajali ne kawai, ƙidãyãwa
  85. A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma
  86. Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa
  87. Ba su malakar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama
  88. Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã
  89. Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni
  90. Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu
  91. Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama
  92. Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã
  93. Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã
  94. Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya
  95. Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai
  96. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so
  97. Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma
  98. Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu