23.The Believers

  1. Lalle ne, Mũminai* sun sãmi babban rabõ
  2. Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne
  3. Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne
  4. Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne
  5. Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne
  6. Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne
  7. Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi
  8. Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne
  9. Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa
  10. Waɗannan, sũ ne magãda
  11. Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi,* su a cikinta madawwama ne
  12. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka
  13. Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya
  14. Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyawun mãsu halittawa
  15. Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne
  16. Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar alkiyãma, za a iãyar da ku
  17. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba
  18. Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne
  19. Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci
  20. Da wata itãciya,* tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ
  21. Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni* mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ
  22. Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku
  23. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba
  24. Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko
  25. Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci
  26. Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka taimakeni Saboda mutãnena sun ƙaryatã ni
  27. Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idon Mu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne
  28. Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai
  29. Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa
  30. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙiƙa' Mãsu jarrabãwa
  31. Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu
  32. Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba
  33. Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã
  34. Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne
  35. Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da kasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne
  36. Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi
  37. Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa,* kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba
  38. Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba
  39. Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni
  40. Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma
  41. Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai
  42. Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu
  43. Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba
  44. Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni
  45. Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyin Mu da, dalĩli bayyananne
  46. Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya
  47. Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne
  48. Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku
  49. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu* zã su shiryu
  50. Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã* Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari
  51. Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi* kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne
  52. Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa
  53. Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu,* kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su
  54. To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci
  55. Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya
  56. Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri
  57. Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu
  58. Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni
  59. Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki
  60. Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu
  61. Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri)
  62. Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su
  63. Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su, mãsu aikatãwa ne
  64. Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa
  65. Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku
  66. Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya
  67. Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha
  68. Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu
  69. Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi
  70. Kõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne
  71. Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton* (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa
  72. Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa
  73. Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya
  74. Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne
  75. Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa
  76. Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba* sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u
  77. Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi
  78. Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa
  79. Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku
  80. Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba
  81. Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa
  82. Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lale ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne
  83. Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko
  84. Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani
  85. Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba
  86. Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma
  87. Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba
  88. Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani
  89. Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku
  90. Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne
  91. Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa
  92. Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka
  93. Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi
  94. Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai
  95. Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi
  96. Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ ne Mafi sani game da abin da suke siffantãwa
  97. Ka ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu
  98. Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni
  99. Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya)
  100. Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su
  101. Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba
  102. To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo
  103. Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama
  104. Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne
  105. Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa
  106. Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwace ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu
  107. Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci
  108. Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana
  109. Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi
  110. Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõ Na kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya
  111. Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo
  112. Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru
  113. Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa
  114. Ya ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani
  115. Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba
  116. Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja
  117. Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara
  118. Kuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama